Motar mai ta shiga Gaza a karon farko cikin kwanaki 38

Motar ɗaukar mai ta farko ta shiga Zirin Gaza tun bayan da Isra’ila ta hana shigar da mai yankin Falasɗinawa kwanaki 38 da suka gabata.

A safiyar Laraba babbar motar da ke ɗauke da man ta shiga Zirin Gaza daga iyakar Rafah da ke ƙasar Masar.

Kafar yaɗa labaran ƙasar Masar ta ce za a kai mai ne ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya “domin ci gaba gudanar da ayyukan jin kai a yankin Falasɗinawan da ke fama da karancin mai”

Wasu ganau sun bayyana cewa ƙarin wasu manyan motocin dakon mai guda biyu suna jiran tantancewa a iyakar Rafah domin su ma su shiga Gaza.

Rashin man fetur a Gaza ya tsayar da harkokin rayuwa da dama, inda asibitoci suka daina aiki, lamarin da ya yi ajalin ƙananan yara da sauran marasa lafiya asibitoci.

KU KUMA KARANTA: An rufe manyan asibitocin Gaza biyu saboda hare-haren Isra’ila

Mutanen da ke fama da raunuka da cututtuka masu haɗari a Gaza sun shiga halin ha’ula’i kafin daga bisani a ba da izinin fitar da su zuwa wasu ƙasashe domin kula da lafiyar.

Gabanin fara yaƙin Isra’ila da Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, Falasɗinawa sama da 20,000 ne ke zuwa ƙasashen waje domin duba lafiyarsu, ciki har da masu fama da cututtuka irin su kansa da dangoginsu.

Yaƙin Isra’ila kuma ya yi sanadiyyar jikkata dubban mutane a Gaza, ga shi kuma rashin mai a asibitoci ya kawo cikas ga yadda jami’an lafiya ke duba mutane.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *