Motar kamfanin gine-gine ta kashe mutane 4, ta raunata 16 a jihar Kwara

Mutane 4 ne suka mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Oloru zuwa sabuwar Jebba a ƙaramar hukumar Moro a jihar Kwara ranar Juma’a.

Babban kwamandan hukumar FRSC a jihar Kwara, Frederick Ogidan, ya bayyana hakan a garin Ilorin ranar Lahadin da ta gabata cewa motar ta wani kamfanin gine-gine na ƙasar Sin ce mai suna ‘CGC Construction Company’.

Ya ɗora alhakin hatsarin, wanda ya auku a Olooru, sakamakon gudun wuce ƙa’ida.

KU KUMA KARANTA: Mutane 18 sun mutu, 12 sun samu raunuka, sakamakon hatsarin mota a Kano

Mista Ogidan ya ce ‘yan uwan mamatan sun yi iƙirarin gawarwakin mutanen yayin da aka kai waɗanda suka jikkata asibiti a ƙauyen Kambi da ke yankin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *