Wata mota ɗauke da jami’an ‘yan sanda zuwa wurin aiki wacce ta taso daga hedkwatar ‘yan sanda SCID a jihar Kebbi ta samu hatsarin da ya yi sanadin mutuwar wani Sufeto na ‘yan sanda.
A wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce hatsarin ya afku ne a sakamakon fashewar taya.
“An samu mummunan hatsarin mota ɗaya tilo a hanyar Koko/Jega, wanda ya haɗa da motar ‘yan sanda ta Toyota Land Cruiser mai lamba REG. 5465D, ɗauke da tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin AC CID na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ACP Suleiman Saɗe da wasu mutane tara.
A yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ziyarar wani wurin da aka aikata laifi a ƙauyen Kendawa, gundumar Dutsinmari a ƙaramar hukumar Koko/Besse.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 25 a Neja
Lokacin da suka isa yankin NNPC a garin Koko, ɗaya daga cikin tayoyin motar ya fashe kuma motar ta mirgina sau uku a cikin daji da ke kusa.
Nan take tawagar ‘yan sanda daga sashin Koko suka ziyarci inda lamarin ya faru, inda aka kwashe waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Koko domin samun kulawa, inda wani Sufeto Sa’idu Idiya na SCID ya mutu kamar yadda wani Likita ya tabbatar.
Daga bisani an kai gawar tare da sauran waɗanda abin ya rutsa da su zuwa FMC da ke Birnin Kebbi domin ci gaba da yi musu magani.
Allah ya jikan sufeto Sa’id Idiya ya huta a Jannatul Fiddaus, amin. Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada