A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne wata tankar man dizal ta murƙushe wata mata da ba a tantance ba, ta mutu har lahira a gadar Otedola da ke unguwar Berger a jihar Legas.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa babbar motar mai lamba GME 483XD ta rasa yadda za ta yi a cikin gadar da ba ta da tushe ta kutsa cikin motoci guda uku.
Da yake tabbatar da lamarin, babban sakatare na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) Dr Olufemi Oke – Osanyintolu ya ce hatsarin ya faru ne bayan da motar tanka ta samu matsala a lokacin da ta ke motsi.
A cewarsa, “Lokacin da aka isa wurin da lamarin ya faru, an gano cewa wata tankar mai cike da man dizal (lita 60,000) ta murƙushe wata mata mai talla (Hawker) a kan gadar Otedola ta cikin garin Berger.
KU KUMA KARANTA: Mutane huɗu sun mutu, da dama sun jikkata a hatsarin mota a hanyar Ibadan
“Bincike da LRT ta yi ya nuna cewa babbar motar ƙirar mai lamba GME 483XD ta samu matsala ta hanyar tsinkewar birki, kuma ta auka cikin wasu motocin da ke ci gaba da tafiya (suzuki mai lamba EPE_302HR da Toyota camry reg lamba MUS242HM, Avalon AYE 453SF) Motar guda uku tana cikin tsari.
“Rundunar LRT, tare da NPF, LASAMBUS, FRSC, LASTMA jami’an RRS suna nan a ƙasa don ceto lamarin.”
Osanyintolu ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da aikin a wurin da hatsarin ya auku.
A halin da ake ciki, an samu cunkoson ababen hawa a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan sakamakon haɗarin.
[…] KU KUMA KARANTA: Mota ta murƙushe wata mai talla ta mutu har lahira a Legas […]