Mota ta buge wani ɓarawon waya a Kano – ‘Yan sanda

0
113

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce mota ta buge wani mutum da ya yi ƙwacen waya yayin da ya sheƙa a guje domin tsallaka titi a cikin birnin na Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi da maraice.

“Yanzu na samu rahoto daga Zoo Road cewa wani ya zare danbida ya kwaci wayar wata mata. Yana tsallaka titi mota ta kaɗe shi. Ana buƙatar mu kai shi asibiti,” in ji Abdullahi Kiyawa.

Sai dai daga bisani kakakin ‘yan sandan na Kano ya sake wallafa wani saƙo da ya nuna cewa mutumin da ya ƙwaci wayar yana cikin mummunan yanayi.

KU KUMA KARANTA: An kama masu ƙwacen waya 26 a Jigawa

Ya ce: “Bayan mun kai (mutumin da ya ƙwaci waya) asibiti yana ɗan motsi, kashin bayansa ya karye kuma kansa ya fashe”, inda ya ƙara da cewa asibitin suna tunanin kai shi sashen bayar da kulawar gaggawa.

Jihar ta Kano ta yi ƙaurin suna game da matsalar masu ƙwacen waya. Sau da dama sukan kashe mutum ne sannan su ƙwace wayarsa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sha kama masu ƙwacen waya tana gurfanar da su a gaban ƙuliya. Sannan tana fitar da bayanai a-kai-a-kai game da yadda mutane za su kauce wa wannan matsala.

Leave a Reply