Mohamed Bazoum ya yi yunƙurin tserewa — Sojojin Nijar

0
253

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun daƙile wani yunƙuri da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ya yi na tserewa daga ƙasar.

Sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka karanta a gidan talabijin na ƙasar ranar Alhamis da maraice.

Bazoum yana tsare a hannun sojin da suka kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuli duk da cewa ƙasashen duniya sun yi ta kiraye-kirayen sakinsa.

Mai magana da yawun gwamnatin sojin Kanar-Manjo Amadou Abdramane, wanda ya bayyana hakan a jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasar, ya ce Bazoum da iyalansa da taimakon wasu jami’an tsaro, sun kitsa tserewa ta hanyar tuƙa shi zuwa wajen birnin Yamai babban birnin ƙasar, inda daga nan zai shiga jirgi mai sauƙar ungulu zuwa Nijeriya mai maƙwabtaka.

Ya ƙara da cewa Bazoum ya yi ƙoƙarin tserewa da ƙarfe uku na safiyar ranar Alhamis tare da iyalansa da masu dafa masu abinci biyu da kuma jami’an tsaro guda biyu.

KU KUMA KARANTA: Amurka ta soke tallafin dala miliyan 442 da take ba wa Nijar

“Matakin gaggawa da jami’an tsaro suka ɗauka ya sa sun iya daƙile yunƙurin wanda aka shirya shi don kawo ruɗani a ƙasarmu,” in ji Kanar-Manjo Abdramane.

Sai dai ba a ji martani daga ɓangaren hamɓarar Shugaba Bazoum ba, wanda har yanzu ba a san inda yake ba.

Juyin mulkin da aka yi a Nijar shi ne na biyar a yankin Yammacin Afirka a cikin shekara uku.

Kamar yadda aka hamɓarar da zaɓaɓɓun shugabanni a Mali da Burkina Faso, sojoji sun ce sun hamɓarar da Bazoum ne saboda ci gaba da ƙaruwar rashin tsaro da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane a yankin, wanda sojojin suka ce za su iya magancewa fiye da gwamnatin farar hula.

’Yan jam’iyyar Bazoum da iyalansa sun ce an yanke masa ruwa da wutar lantarki, abin da ya jawo Allah-wadai daga ƙasashen yammacin duniya, tsofaffin ƙawayen Nijar.

Leave a Reply