Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargaɗi game da yiwuwar watsuwar rikici a Gabas ta Tsakiya a yayin da Amurka ke matsa ƙaimi wurin kai hare-hare kan ƙungiyoyin da Iran take goyon baya.
“Idan kana wasa da wuta, mai yiwuwar wutar ta zama tamkar gobara wadda ba za a iya shawo kanta ba. Muna fuskantar hatsari, kuma akwai babbar barazana ta yiwuwar gaza shawo kan abin da zai faru,” a cewar Fidan a wata hira da gidan talbijin na ƙasa ranar Lahadi.
Fidan ya ce Turkiyya tana tattaunawa da Amurka da sauran ƙasashen da ke yankin a-kai-a-kai , yana mai ƙarawa da cewa: “Akwai buƙatar mu guje wa watsuwar rikicin zuwa wasu sassan yankin. Halin da ake ciki ba mai kyau ba ne. Za mu iya fuskantar watsuwar rikicin sosai.”
KU KUMA KARANTA: Turkiyya za ta ci gaba da fallasa farfagandar Isra’ila – Altun
Da yake magana game da masu bijiro da batun tsaron Isra’ila a koyaushe, Fidan ya ce babban abin da Isra’ila ta sanya a gaba shi ne fadada iyakokinta maimakon tsaronta.
Isra’ila za ta samu zaman lafiya ne idan ta daina “shirga karga” ga ƙasashen duniya sannan ta bari Falasɗinawa suka samu kasa mai ƴancin kanta, a cewar ministan harkokin wajen na turkiyya.
Fidan ya jaddada tunatarwa ga kasashen yankin waɗanda suka sha alwashin cewa a shirye suke su ɗauki nauyin tabbatar da zaman lafiya, inda ya ce: “Lokacin da muka bijiro da batun samar da ƙasashe biyu masu ƴancin kansu, babban burinmu shi ne mu kasance masu shiga tsakani wajen tabbatar da hakana.”