Ministan tsaron Badaru ya halarci babban taron ƙungiyar ‘yan kasuwa ta ƙasa a Kwara

0
232
Ministan tsaron Badaru ya halarci babban taron ƙungiyar 'yan kasuwa ta ƙasa a Kwara

Ministan tsaron Badaru ya halarci babban taron ƙungiyar ‘yan kasuwa ta ƙasa a Kwara

Daga Idris Umar, Zariya

Mai girma ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, CON, MNI, a yau Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025, ya halarci babban taron ƙoli na ƙungiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da harkokin noma ta ƙasa, Chambers of Commerce, Industry, Mines and Agriculture (NACCIMA), wanda aka gudanar a garin Ilorin na Jihar Kwara.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Tarayya zata haɗa hannu da Gwamnatin Jihar Kano domin gina cibiyar kasuwanci ta zamani

A jawabin da ya gabatar a wajen, minista ya ja hankalin ƴaƴan ƙungiyar da su zuba jari a masana’antar samar da kayayyakin aikin tsaro ta ƙasa, a ƙoƙarin da shugaban ƙasa Tinubu ke yi na kawo managartan sauye-sauye a fannin. Ya ƙara da bayyana irin da rawar da ƴan kasuwa za su taka wajen bunƙasa fannin tsaron ƙasar musamman ta ɓangaren samar da kayan aiki na cikin gida, ƙirƙire-ƙirƙire da haɗin gwiwar samar da tsare-tsaren aiki.

Taron ya samu halartar muhimman mutane da suka haɗa da ƙaramin ministan kasuwanci, Sanata John Owan Enoh, wanda ya wakilci shugaban ƙasa Tinubu, da kuma ministan ciniki da masana’antu, Dakta Olajumoke Oduwole, da ministan shari’a na ƙasa, Lateef Fagbemi SAN, da mataimakin gwamnan Jihar Kwara, Kayode Alabi wanda ya wakilci gwamnan Jihar.

Leave a Reply