Ministan babban birnin tarayyar ya ƙaddamar da yaƙi da mabarata

0
31
Ministan babban birnin tarayyar ya ƙaddamar da yaƙi da mabarata

Ministan babban birnin tarayyar ya ƙaddamar da yaƙi da mabarata

A jiya litinin ne Ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike ya ƙaddamar da yaƙi da mabarata, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro za su fara kama su daga yau idan sun sake fitowa bara a titunan babban birnin.

To sai dai Ƙungiyar Masu Larura ta Musamman ta Ƙasa ta ce za ta ƙalubalanci wannan doka a kotu idan haka ya faru, akan ko mene ne dokar ƙasa ta ce a game da ‘yancin mabarata.

Shugaban Kungiyar, Kwamred Yarima Suleiman ya ce ƙungiyar za ta ɗauki mataki domin Ministan bai zauna da su ba, kuma bai tuntuɓi Hukumar Kula Da Masu Larura ta Musamman ba.

Yarima ya ce abin da ya kamata Minista ya yi shi ne, ya yi wa masu larura ta musamman tanadin abubuwa masu tsoka kamar a basu bashi domin su yi kasuwanci, ko kuma a gina su ta fannin koyar wasu sana’o’i, ko kuma a wadata su da abinci ko hanyan samun abincin cikin sauƙi.

Yarima ƙara da cewa suna nema Minista ya janye mugun kalma na ‘Informant” da ya lankaya masu, saboda yana iya sawa ‘ya’yansu, suyi kyamarsu, ko kuma waɗanda ke taimaka masu su kyamace su ko ƙungiyar ta ɗauki mataki kan kalaman Ministan.

Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ya ce birnin ya zama kaman birnin mabarata, kuma wannan abin kunya ne a gare mu.

Wike ya ce duk lokacin da baƙi suka shigo garin, babu abin da suke fara karo da shi sai mabarata a titunan birnin, saboda haka daga yau Litinin 28 ga watan Oktoba jami’an tsaro da sauran ma’aikatan birnin za su fara ɗiban mabarata daga kan titunan Abuja.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta ba da kwangilar fara gyaran titin Abuja zuwa Tafa

Wike ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunta ba, domin wasu mabarata suna baiwa ‘yan ta’adda labarai, wato abin da ake cema ‘Informant’ a turance.

To ko mene ne kundin tsarin mulki ya tanada kan wannan hukunci da Ministan ya ɗauka?

Barista Mustapha Haruna Soba ya yi fashin baƙi cewa kundin tsarin mulki ya ba mabarata dama na yin walwala a ko ina a cikin ƙasar, saboda haka mabarata suna iya shigar da ƙara a kotu inda za su ƙalubalanci wannan tsari da Minista Nyesome Wike ya ɓullo da shi.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya idan har Ƙungiyar Masu Larura ba su shirya da Minista Nyesome Wike ba.

Leave a Reply