Minista ya faɗi dalilin da ya sa ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu

0
156

Ministan ƙwadago da ɗaukar ma’aikata, Simon Lalong ya yi murabus daga kujerarsa a hukumance a ranar Talata, 19 ga watan Disamba.

A cewar wata sanarwa daga kakakinsa, Simon Macham, Lalong ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu Legit Hausa ya wallafa.

Ya ɗauki matakin ne domin ya samu damar ɗarewa kujerarsa a matsayin sanata mai wakiltan Filato ta kudu karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Lalong ya yi murabus ne sakamakon nasarar da ya samu a zaɓen sanata na ranar 25 ga watan Fabrairu, bayan kotun ɗaukaka ƙara ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen a ranar 7 ga watan Nuwamba.

Hukuncin kotun ya sauya sanarwar da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ta yi a baya, inda ta ayyana Napoleon Bali na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Lalong ya karɓi takardar shaidar cin zaɓe daga wajen INEC a watan jiya sannan a yanzu ya shirya kama aikinsa na sanata.

Mista Macham ya jaddada cewa zabin ministan na sauka daga mukaminsa na minista abu ne mai matukar nauyi.

Ba a ɗauki wannan mataki da wasa ba saboda amana da ƙwarin gwiwar da Shugaba Tinubu ya ba shi.

A baya ministan ya yi aiki a matsayin darakta janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima, inda ya taka muhimmiyar rawar gani wajen nasarar da APC ta samu.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta nakalto, sanarwar na cewa:

Sai dai kuma, bayan tuntuɓa mai yawa da mai girma shugaban ƙasa da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummata, ya zama dole gareni in ci gaba da zama a majalisar dattawa don ci gaba da ba da gudummawa ga ajandar sabunta fata na gwamnatin ka da kuma ci gaban dimokuraɗiyyar mu gaba ɗaya.”

Mista Lalong ya yi godiya ga shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin aiki a majalisarsa da kuma irin goyon baya da jagorancin da ya samu a lokacin da yake rike da muƙamin minista.

Yayin da yake a majalisar dattawa, ministan ya yi alƙawarin biyayya, goyon baya, da bayar da haɗin kai ga shugaba Tinubu, domin bayar da gudumawa ga ajandar sabunta fata da kuma ciyar da manufofin jam’iyyar APC gaba don samun haɗin kai, ci gaba da wadata a Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa sabon zaɓaɓɓen Sanatan ya ziyarci majalisar ne domin miƙa takardar shaidar cin zaɓensa da kuma takardun da suka dace ga magatakardar majalisar.

Leave a Reply