Me shugaba Tinubu ya faɗa kan nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa a kotun ƙolin Najeriya?

0
162

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya bayyana jin daɗi da farin cikinsa tare da yin maraba da hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke a kan zaɓen shugaban ƙasar, inda ta tabbatar da nasararsa.

A ranar Alhamis ne Kotun ƙolin mai tawagar alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a John I. Okoro ta yanke hukuncin da ya zama na ƙarshe a kan zaɓen shugaban Nijeriya wanda Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour ke ƙalubalanta.

“Kotun ta yi adalci ga dukkan batutuwan da aka gabatar mata duba da hurumin doka, ba tare da jin tsoro ko fifita wani ba, in ji Shugaba Tinubu, a sanarwar da fadarsa ta fitar jim kaɗan bayan hukuncin kotun.

“Babu tantama, a wannan hukunci na yau, an sake ƙarfafawa tare da daga martabar ingancin zaɓe da dimokuraɗiyyarmu mai aiki da kundin tsarin mulki. An kuma ɗabbaka wannan tsarin a ƙimar siyasarmu saboda nutsuwa da ƙwarewar Mai Girma Mai Shari’ar da ya shugabanci yanke hukuncin ƙarshe na wannan shari’a.”

Shugaban na Nijeriya ya kuma ce a yayin da wannan hukunci ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen waye ya lashe zaɓen Shugaban ƙasa na 2023, kuma ya cika ƙa’idojin da kundin tsarin mulki ya sharɗanta, “Ina so na sake jaddada imanina ga tsarin shari’a na ƙasarmu wanda ban taɓa tantama game da shi ingancinsa ba.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’a albashin watannin da suka yi suna yajin aiki

“Saboda na san kotunanmu ba za su gaza yin adalci ga dukkan ‘yan Nijeriya ba kan kowanne batu kuma a kowane lokaci.

“Yau an sake tabbatar da cewa jam’iyyata ta APC ce ta yi nasarar zaɓe tare da rinjayen ƙuri’un da ‘yan Nijeriya suka jefa.”

Shugaba Tinubu ya kuma ce “Tare da ɗimbin godiya ga Allah Mabuwayi, na karɓi wannan hukunci na yau cikin ƙanƙan da kai, tare da buri da buƙatar fuskantar ƙalubalen da ke damun al’ummarmu.”

Da yake ƙira ga dukkan ɓangarori kan su zo a haɗa kai a gina Nijeriya, Tinubu ya ce “Dukkanmu ‘yan gida ɗaya ne, kuma wannan lokaci na buƙatar mu ci gaba da aiki don gina ƙasarmu tare.

Ƙarfin bambance-bambancen da ke tsakaninmu da girman ƙasarmu da ta haɗa mu waje guda, za su tirsasa mana wajen karkatar da al’ummarmu ga gina ƙasa mai ƙarfi, yalwar arziƙi da albarka.

Ya ce “A shirye nake da na karɓi duk wata gudunmawa daga kowanne ɗan Nijeriya don haɓaka ci gabanmu baki ɗaya.”

Tinubu ya kuma miƙa godiyarsa ga dukkan ‘yan Nijeriya bisa damar da suka ba shi na hidimtawa ƙasarsu.

Ya yi alƙawarin zai biya buƙatunsu da ma yin sama da yadda suke tsammani a ɓangarorin hidimtawa da tabbatar da kyakkyawan shugabanci.

Bayan zaɓen Shugaban ƙasa a Nijeriya ne ‘yan takarar jam’yyun PDP Atiku Abubakar da na LP Peter Obi suka garzaya kotun ƙararrakin zaɓe tare da ƙalubalantar nasarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bawa Tinubu.

Leave a Reply