Connect with us

Laifi

Mayaƙan Boko Haram sun sace mata 319 a Borno

Published

on

Rahotanni sun ce mayaƙan Boko Haram sun yi awon gaba da wasu mata 319 ‘yan gudun hijira a garin Ngala da ke Ƙaramar Hukumar Gambarou Ngala ta Jihar Borno.

Wata majiya a sansanin gudun hijira na Babban Sansani ta ce mayaƙan na Boko Haram sun sace matan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa daji domin ɗebo itacen girki a ranar Lahadin da ta gabata.

Majiyar ta ce ’yan ta’addan sun yi wa matan ƙawanya ne a dajin Bula Kunte da ke Yammacin garin Ngala.

“Sun kyale tsofaffin da ke cikinsu sannan suka shiga daji da sauran ’yan mata 319 da kuma wasu samari.

“Amma, uku daga cikin ‘yan matan da suka tsere suka koma Ngala sun ce masu tayar da ƙayar bayan sun kai su wani daji kusa da ƙauyen Bukar-Mairam a Jamhuriyyar Chadi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, sun ƙona mutane da ransu

“Cikin duhun dare ’yan matan suka tsere bayan mayaƙan sun kwanta barci, inda suka shafe tsawon kwanaki biyu suna tafe a ƙasa kafin su isa Ngala.

“Yawancin ‘yan matan da lamarin ya rutsa da su sun fito ne daga sansanin Babban Sansani sauran kuma daga sansanin Zulum da Arab.

“Duk ’yan matan sun shiga jeji ne domin ɗebo itacen da suke sayarwa da kuma girkin abinci saboda wanda muke samu a sansanin ba ya wadatar da mu. Rayuwa tana da wahala a nan,” in ji shi.

Sai dai wata majiyar tsaro da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta shaida wa Aminiya cewa, adadin matan da mayaƙan suka sace 113 ne.

“Labarin da muka samu shi ne cewa an sace mata 113 amma ba su kai 319 da ake ikirari ba.”

Kazalika, wata majiyar jami’an tsaron ta ce sun sha gargadin ‘yan gudun hijirar kan zuwa wasu yankuna a cikin daji saboda fargabar kai hari ko kuma faruwar irin hakan.

“A koda yaushe muna gargaɗin da su riƙa kai-komo a wurare masu aminci, amma matsin tattalin arziki ne ke sa akasarinsu shiga wasu wurare masu hatsari.

“Saboda ba su da wata hanyar dogara da kai da ta wuce ɗebo itacen a matsayin sana’a.

“A yanzu ana sayar da ƙaramin kwanon garin masara kan Naira 2,200, saboda haka a ina za su samu kuɗin siya.?

“Wannan yanayi da ake ci ya sanya ba za mu iya hana su neman abin dogaro da kai ba idan har mu ba za mu iya ciyar da su ba,” inji shi.

Wannan dai na ɗaya daga cikin manya-manyan sace-sacen da aka yi a Borno, tun bayan sace ’yan mata 276 na Sakandaren Chibok da aka yi a ranar 14 ga watan Afrilun 2014.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Laifi

‘Yan bindiga sun sace ‘yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

Published

on

'Yan bindiga sun sace 'yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

‘Yan bindiga sun sace ‘yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

Daga Idris Umar, Zariya

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan jarida biyu a ƙauyen Danhonu da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kai hari a cikin al’umma a daren ranar Asabar inda suka yi awon gaba da ‘yan jarida biyu da iyalansu.

Waɗanda abin ya shafa, Alhaji AbdulGafar Alabelewe da AbdulRaheem Aodu, ‘yan jarida ne na jaridun The Nation da Blueprint a jihar Kaduna, bi da bi.

Alabelewe wanda shi ne shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), majalisar jihar Kaduna a halin yanzu, an dauke shi tare da matarsa da ‘ya’yansa biyu.

An kuma yi garkuwa da Aodu da matarsa, inda suka bar ‘yarsu da ba ta da lafiya.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a jihar Delta

Da yake bayyana hakan, Taofeeq Olayemi, dan uwa na daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, ya ce ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar ne da misalin karfe 10:30 na dare, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su yi awon gaba da su.

Da farko ‘yan fashin sun tafi da Alabelewe, matarsa, ‘ya’yansa uku, da kuma wani bako, amma daga baya suka sako yarinyar daya daga cikin yaran.

“Sun shiga gidan Abdulgafar ta katanga.

“Sun shiga cikin ɗakin kwanansa kai tsaye suka ɗauko shi da matarsa da ‘ya’yansu biyu suka tafi nan take, inda ‘yan banga suka iso suka fara harbin iska,”

Ya zuwa haɗa wannan rahoton babu ɗuriyar duk wanɗana aka sacen.

Tuni kunyar ‘yan jaridar ta jihar Kaduna ta sanar tare da tabbatar da faruwar lamarin.

Continue Reading

Laifi

Wani matashi ya kashe mahaifinsa a Delta

Published

on

Wani matashi ya kashe mahaifinsa a Delta

Wani matashi ya kashe mahaifinsa a Delta

Ana zargin wani matashi mai suna Ufuoama Umurie ya kashe mahaifinsa a Unguwar Okpare da ke Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, ranar Laraba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an tsinci gawar mahaifin mai suna Rabaran Isaac Umurie, wanda ɗaya ne daga cikin limaman cocin St. John’s Anglican da ke Okpare-Olomu a safiyar wannan Larabar.

Bayanai sun ce tun farko lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na tsakar dare, inda wanda ake zargin ya kori mahaifiyarsa a lokacin da take ƙoƙarin ceto rayuwar mijinta amma ita kanta da ƙyar ta tsira.

Ufuoma, wanda a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda, an ce ya yi amfani da laujen yankar ciyawa ya yanka mahaifinsa sannan ya sassare shi a sassan jikinsa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa

Rahotanni sun ce matashin ya yi wa mahaifinsa wannan aika-aikar ce a lokacin da yake barci kafin maƙwabta da mabiya cocin su su kawo ɗauki.

Duk da cewa har yanzu ba a gano abin da ya haddasa faruwar lamarin ba, wasu mazauna unguwar yankin sun yi zargin cewa Ufuoma yana fama da taɓin hankali, kuma wannan ne karo na biyu da ya kai wa mahaifin nasa hari.

Continue Reading

'Yan bindiga

‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa

Published

on

'Yan bindiga sun kashe malamin jami'a a Katsina, sun sace 'ya'yansa

‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa

Rahotanni daga Jihar Katsina  na cewa ‘yan bindiga sun kashe wani malamin Jami’ar Tarayya ta Dutsinma.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da tsakar dare da misalin ƙarfe 1:30 inda ‘yan bindigar suka afka gidan Dakta Tiri Gyan da ke Yarima Quarters a Ƙaramar Hukumar Dutsinma.
Mai magana da yawun ‘yan sandan  reshen Katsina Abubakar Sadiq ya tabbatar wa kafar watsa labarai ta Channels  da kisan malamin.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka gidan malamin jami’ar da makamai daban-daban inda suka yi ta harbi domin tsorata mazauna rukunin gidajen.

Sun kuma bayyana cewa ɓarayin sun sace yara biyu na Dakta Gyan a lokacin da suka kai harin.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun sace Hakimi da manoma 2 a Kaduna

Kashe malamin na zuwa ne mako guda bayan kashe mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sokoto Farfesa Yusuf Saidu.

An kashe shi a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Sokoto.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like