Mayakan Al-Qassam Brigades, wato ɓangaren soji na ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas, sun harba manyan rokoki daga Zirin Gaza zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila da garuruwan da ke kewayensa da sanyin safiyar Litinin, abin da ya sa jiniya ta yi ta kuka.
Gidan rediyon Rundunar Sojin Isra’ila ya ce haka kuma an harba rokoki a biranen Rishon Lezion, Lod, Ramla, Bnei Brak da Sderot baya ga wani matsugunin Yahudawa mai suna Modi’in Illit da ke tsakiyar Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
A wani sako da suka wallafa a manhajar Telegram, mayaƙan Al-Qassam Brigades sun tabbatar da cewa sun harba bama-bamai a Tel Aviv da kewayensa.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun yi artabu da mayaƙan Hezbollah
“Al-Qassam Brigades na yin luguden wuta da makaman roka samfurin M90 a birnin Tel Aviv da kewayensa domin yin raddi ga kisan kiyashin da Yahudawa suke yi wa fararen-hula,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta nuna bidiyoyin harin rokokin da ƙungiyar ta kai.
Babu bayani kan ko hare-haren sun yi sanadin mutuwa ko jikkatar wani ko wasu.