Matsalar tsaro da ambaliyar ruwa ta sa manoma dubu 46 sun rasa muhallansu a Neja

0
48
Matsalar tsaro da ambaliyar ruwa ta sa manoma dubu 46 sun rasa muhallansu a Neja

Matsalar tsaro da ambaliyar ruwa ta sa manoma dubu 46 sun rasa muhallansu a Neja

Jimillar manoma 46, 853 daga gidaje 5, 863 ne suka rasa muhallansu sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji da ta’addanci da ambaliyar ruwa da rikicin makiyaya da manoma a faɗin jihar Neja.

Wani rahota da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja ta samu ya nuna cewa wasu daga cikin manoman sun rasa muhallansu sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji tun 2018.

Bayanan sun nuna cewa manoman da abin ya shafa sun haɗa da maza 5,863 da mata 23, 450 da ƙananan yara 17, 740.

KU KUMA KARANTA:Mutum 5 sun rasu a Neja sakamakon rikicin manoma da makiyaya

Hukumar ta ce akwai ‘yan gudun Hijrah 5, 823 a sansanin ‘yan gudun Hijrah na Gwada da ya hada da maza 970 da mata 2, 051 da kananan yara 2, 802.

A sansanin ‘yan gudun Hijrah na Kuta, hukumar NSEMA ta bayyana cewa akwai manoma ‘yan gudun Hijrah 3, 180 wadanda ya hada maza 530 da mata 1, 040 da kananan yara 1, 610 inda ta ce an bude dukka sansanonin a 2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here