Matsalar ruwan sha a Warawa ta jihar Kano, har ya kai ga suna shan ruwan da Karnuka ke Wanka
Daga Jamilu Lawan Yakasai
A ƙaramar hukumar Warawa ta Jihar Kano, mazauna yankin na fuskantar babbar matsala ta rashin tsaftataccen ruwan sha, musamman a lokacin azumin watan Ramadan. Jama’a sun bayyana cewa, ruwan da karnuka ke wanka a ciki, suna amfani da shi wajen sha da sauran bukatun yau da kullum.
Rahotanni sun nuna cewa, matsalar ba ta tsaya a Warawa kadai ba. Daga cikin kauyukan da ake fuskantar wannan matsala sun haɗa da Dakata, Abdallawa, Kanwa, Madari, Juma, da kuma cikin garin Warawa.
Wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa: “Mun dade muna amfani da wannan ruwan saboda babu wani madadin da muke da shi sama da shakarau 30.
Amma matsalar da muke fuskanta ita ce yadda dabbobi ke shiga cikin ruwan suna wanka da sha, sannan mu kuma muke amfani da shi domin rayuwarmu.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta hana sayar da ruwan jarkoki a faɗin jihar
Wannan matsala tana janyo cututtuka irin su gudawa, zazzabin cizon sauro da na typhoid ga mutanen yankin. Wasu mazauna sun roki hukumomi su kawo dauki ta hanyar samar da rijiyoyi ko tsaftace ruwan domin kare lafiyar su.
Mazauna Warawa suna roƙon mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da samun ingantaccen ruwan sha. Wannan mataki zai taimaka wajen rage yaduwar cututtuka da kuma inganta rayuwar al’umma a wannan yanki.
Domin ceton rayuka da kuma inganta lafiyar jama’a a ƙaramar hukumar Warawa da makwabtanta