Matsalar ƙarancin abinci za ta ta’azzara a Sudan saboda fari — MƊD

0
194

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa abinci zai ƙara ƙaranci a watanni masu zuwa a daidai lokacin da Sudan ke shiga watannin ƙarancin abinci.

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya FAO ta yi gargaɗi a Geneva cewa irin ɓarnar da farin ɗango suka yi wa amfanin gona ya yi matuƙar haddasa matsaloli tun daga tsakiyar shekarar da ta gabata.

Mataimakin wakilin FAO a Sudan Adam Yao ya yi gargaɗi kan cewa matsalolin farin ɗangon sun kai wani “mataki na barazana”, kuma ba tare da tsare-tsare masu ɗorewa ba na daƙile bazuwarsu ba, za a ci gaba da tafka asara.

Wannan na faruwa ne sakamakon rashin ayyukan sa ido a tsakiya da yammacin Sudan sakamakon yaƙin da ake gwabzawa tsakanin sojojin ƙasar da kuma dakarun RSF.

KU KUMA KARANTA: Tallafin abinci na ‘yan gudun hijirar Sudan a Chadi yana dab da ƙarewa – MƊD

A wani ɓangaren, jami’an da ke sa ido kan farin ɗango tare da goyon bayan FAO sun yi ƙoƙarin sa ido kan sama da kadada 113,500 da kuma aiki a kan kadada 23,000 wadda farin suka yi wa ɓarna.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana ƙiyasin cewa mutum miliyan 18 suna fama da ƙarancin abinci – wanda hakan ke nufin an samu ƙarin mutum miliyan goma fiye da bara.

Hukumomin bayar da agaji sun yi ƙoƙarin kai kayan agaji ga mutum miliyan bakwai a Sudan tun daga Afrilun bara.

Leave a Reply