Matatar Ɗangote ta fitar da motoci 1,000 don fara rarraba man fetur kai tsaye ga jihohin Najeriya

0
160
Matatar Ɗangote ta fitar da motoci 1,000 don fara rarraba man fetur kai tsaye ga jihohin Najeriya

Matatar Ɗangote ta fitar da motoci 1,000 don fara rarraba man fetur kai tsaye ga jihohin Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

A yau Litinin ne Matatar Dangote za ta fitar da motoci sama da 1,000 masu amfani da iskar gas dauke da man petur, a matakin farko na shirin rarraba man kai tsaye zuwa jihohi.

A bangarenta kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta ce ta shirya tsaf domin karɓar motocin man a tashoshinta daban-daban da ke a fadin Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Rikici ya ɓarke a tsakanin matatar man Ɗangote da ƙungiyar ma’aikatar mai da iskar gas ta ƙasa NUPENG

masu ruwa da tsaki a matatar man ta Dangote sun shaidawa manema labarai cewa za’a fara rarraba man kai tsaye a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekara guda cif da fara samar da fetur daga matatar.

Leave a Reply