Matatar man Ɗangote ta ƙaryata batun korar ma’aikata

0
245
Matatar man Ɗangote ta ƙaryata batun korar ma'aikata
Shugaban rukunin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote

Matatar man Ɗangote ta ƙaryata batun korar ma’aikata

Daga Jameel Lawan Yakasai

Matatar man fetur ta Dangote ta karyata rahotannin da ke cewa ta sallami ma’aikata, tana mai cewa gyaran tsarin aiki kawai take yi domin kare masana’antar daga ayyukan zagon ƙasa da kuma inganta tsaro da dorewar aiki.

A cikin sanarwar da ta fitar a wannan Juma’ar, matatar ta bayyana cewa sauyin tsarin ya zama dole bayan gano matsalolin tsaro da kuma wasu kura kurai da ke rage ingancin aiki.

Kamfanin ya ce manufar gyaran ita ce kare rayuka da kadarorin ƙasa, tare da tabbatar da cewa masana’antar na ci gaba da amfanar da ƴan Najeriya, kasashen Afirka da ma’aikatanta.

KU KUMA KARANTA: Rikici ya ɓarke a tsakanin matatar man Ɗangote da ƙungiyar ma’aikatar mai da iskar gas ta ƙasa NUPENG

Matatar ta kuma jaddada cewa sama da ma’aikata 3,000 ƴan Najeriya na ci gaba da aiki, inda ƙaramin kaso ne wannan sauyin ya shafa.

Ta ce tana ci gaba da ɗaukar sabbin ma’aikata ta hanyar horaswa da shirin ɗaukar ƙwararru, tare da bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da ƴancin ma’aikata shiga ƙungiyoyin ƙwadago.

Leave a Reply