Matatar fetur ɗin Ɗangote ta fara samar da dizel da man jirgin sama

0
138

Matatar fetur ta hamshaƙin ɗan kasuwar nan na Najeriya Alhaji Aliko Ɗangote ta soma samar da dizel da man jiragen sama.

Wata sanarwa da Rukunin Kamfanonin Ɗangote ya fitar ranar Juma’a ta ce matatar ta bayyana “matuƙar farin ciki” na fara gudanar da wannan aiki da zai bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya da ma sauran ƙasashen Afirka.

“Matatar man tana iya yin lodin tankokin mai 2,900 a kowace rana. Man da matatar za ta samar zai dace da dokokin kare muhalli. An gina matatar ne bisa dokokin Bankin Duniya da Hukumar Kare Muhalli ta Amurka da ta Turai” na rage gurɓata muhalli.

Ɗangote ya gode wa shugaban Najeriya Bola Tinubu da gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kan da ya samu wajen aiwatar da wannan gagarumin aiki.

KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya ba da tallafin karatu ga al’ummar da ya gina kamfani a yankinsu

“Wannan babbar rana ce ga Najeriya. Muna matukar farin cikin kai wa wannan babban matsayi. Wannan babbar nasara ce ga ƙasarmu domin kuwa ta nuna azamarmu wajen aiwatar da manyan ayyuka. Wannan zai kawo gagarumin sauyi a ƙasarmu,” in ji sanarwar.

A watan Mayun 2023 aka ƙaddamar da matatar man ta Ɗangote a wani gagarumin biki da ya samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da dama.

Alhaji Aliko Ɗangote ya ce matatar man fetur ɗin za ta samar da “dubban” ayyukan yi ga matasan ƙasar.

Bayanan da kamfanin Ɗangote ya fitar sun nuna cewa matatar ita ce ɗaya tilo da ke da rariya mafi girma a duniya da za ta iya tace gangar mai 650, 000 a kullum.

Leave a Reply