Matashi ya yi wa ’yar shekara 62 fyaɗe a Borno 

Dubun wani matashi mai shekara 37 ta cika bayan da ya yi wa wata tsohuwa ’yar shekara 62 fyaɗe a Jihar Borno.

Matashin wanda yanzu haka yake komar ’yan sanda ya kuma sace wa dattijuwar kuɗi, bayan da ya yi mata fyaden a ƙauyen Panshani, gundumar Gasi da ke ƙaramar Hukumar Shani ta jihar.

An kama wanda ake zargin ne bayan ɗan uwan dattijuwar ya kai ƙara wurin ’yan sanda cewa tsohuwar mai shekara 62 na komawa gida daga unguwa ne matashin ya tare ta a hanya “ya yi mata fyaɗe, ya kwashi kuɗi naira dubu arba’in da biyu da ɗari bakwai a aljihunta.

KU KUMA KARANTA: Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta

“Don haka yanzu haka ana ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala za a miƙa shi gaban ƙuliya don fuskantar hukuncin da ya yi dai-dai da shi,” in ji Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Yusufu.

Ya ƙara da cewa a cikin watanni ukun da suka gabata rundunar ta kama mutane aƙalla 500 kan aikata laifuka daban-daban a sassan jihar, kuma yawancinsu an miƙa su gaban ƙuliya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *