Matashi ya kashe mahaifiyarsa a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana neman wani matashi ruwa a jallo, wanda ake zargi da caccaka wa mahaifiyarsa wuƙa a kanta da ƙirjinta da sauran sassan jiki.

Da yake tattaunawa da BBC, kakakin ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin mai shekara 22, ya tsere bayan caccaka wa mahaifiyar tasa mai shekara 50 wuƙa.

Ya ce ‘yan sanda sun yi nasarar gano wuƙar da aka yi aika-aikar da ita a unguwar Rimin Keɓe da ke wajen birnin Kano.

KU KUMA KARANTA: Matashi ɗan shekara 24 ya kashe abokinsa a Enugu

Da yammacin ranar Laraba ne matashin da ake zargi ya aikata kisan kan ga mahaifiyarsa wadda a yanzu ba sa tare da mahaifin nasa.

A cewarsa, tuni sun baza koma inda suke ci gaba da neman matashin domin kama shi.

“Mutane na ci gaba da yaɗa cewa an taɓa kai shi (asibitin masu taɓin hankali da ke) Dawanau, amma dai mu muna ci gaba da aikinmu,” in ji SP Abdullahi Kiyawa.


Comments

2 responses to “Matashi ya kashe mahaifiyarsa a Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *