Matashi ɗan shekara 17 ya kashe kansa a Bauchi

2
348

Wani matashi ɗan shekara 17 mai suna Master Betwom Bitrus mazaunin Bombar da ke ƙaramar hukumar Ɓogoro a jihar Bauchi, an zargi shi da kashe kansa.

Jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin Mista Simon Vandi ne ya tabbatar wa manema labarai wannan mummunan lamari, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

A cewar rahoton ‘yan sanda, marigayi Betwom, tare da abokansa, ya je rafin Bombar zuwa yin wanka da yammacin Talata kafin lamarin ya faru.

An ruwaito DPO ɗin yana cewa, “Ina tabbatar muku da misalin ƙarfe 12 na daren yau (Laraba), ofishina ya samu rahoton kashe kansa da wani matashi mai suna Master Betwom Bitrus ɗan shekara 17, mazaunin Bombar a nan garin Ɓogoro ya yi. ”

Ya ƙara da cewa, “Bincike ya nuna cewa yana tare da abokansa jiya (Talata), da yamma. Babu wanda ya san dalilin da ya sa ya rataye kansa.

KU KUMA KARANTA: DSS sun cafke matashin malamin nan Malam Baffa Hotoro a jihar Kano

An tsinci gawarsa a jikin bishiyar da ya rataye kansa. An kai shi babban asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa.”

DPO ya ci gaba da cewa, har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin da ya haddasa faruwar lamarin, inda ya ce, “Na yi nadamar rasuwar marigayi Betwom Bitrus, kuma ina baƙin ciki da iyalan mamacin.”

Da yake magana kan lamarin, wani mazaunin Bombar, Mista Daniel Haruna ya ce, “Eh, ina so in gaya muku cewa wani matashi ya kashe kansa kuma ba mu san dalilin da ya sa ba.

Muna cikin baƙin ciki a halin yanzu. An gan shi na ƙarshe tare da abokansa jiya (Laraba) da yamma.

Ana ci gaba da ƙoƙarin samun muhimman bayanai daga abokanan da aka gan shi a ƙarshe domin a tabbatar da abin da ya kai ga aukuwar lamarin kamar yadda wata sanarwa da Gomna James, jami’in yaɗa labarai ya fitar.

2 COMMENTS

Leave a Reply