Matasan Arewa na son Gwamnan Neja ya bincika rigimar INCRESE da Sai-Baba bisa zargin LGBT

0
102
Matasan Arewa na son Gwamnan Neja ya bincika rigimar INCRESE da Sai-Baba bisa zargin LGBT

Matasan Arewa na son Gwamnan Neja ya bincika rigimar INCRESE da Sai-Baba bisa zargin LGBT

Matasan Arewa, ƙarƙashin ƙungiyar Gamayyar ƙungiyoyin Matasan Arewa sun yi ƙiran gaggawa ga Gwamna Umaru Mohammed Bago na Jihar Neja da ya bincika dambarwar da ke faruwa tsakanin ƙungiyar INCRESE da wani ɗan gwagwarmaya, Sai Baba.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Rundunar ‘yansanda a jihar Neja ta tsare wani mai fafutuka kuma mai sharhi kan al’amuran zamantakewar al’umma a garin Minna, Muhammad Yahaya Usman, bisa zarginsa da wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya buƙaci a gudanar da bincike kan ayyukan wata ƙungiya mai zaman kanta.

Ƙungiyar, mai suna, Cibiyar Kare Lafiya da Haƙƙin Jima’i ta Ƙasa da Ƙasa, INCRESE, na rajin kare Haƙƙin jima’i ne ga mata.

KU KUMA KARANTA:Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi

Usman, wanda aka fi sani da Sai Baba, ya yi zargin cewa ƙungiyar na yaɗa ayyukan ƙungiyar auren-jinsi ta duniya, LGBT ne kuma ya yi ƙira ga gwamnatin jihar Neja da ta binciki ayyukansu da kuma hanyoyin da su ke samun kuɗaɗen.

A wani saƙo da ya wallafa a Facebook bayan an sake shi, Usman ya ce a maimakon mayar da martani ga batutuwan da ya wallafa, sai ƙungiyar ta shigar da ƙara a kan zargin ɓata masa suna a sashin binciken manyan laifuka na jihar, SCID.

Da ya ke zanta wa da manema labarai a Abuja, Shugaban Ƙungiyar Matasan, Comrade Hamza Saulawa yace “idan babu rami meya kawo rami? shin me yasa ƙungiyar ta tunzura don kawai Sai Baba ya tuhumesu kan aikace-aikacen ta?”

Ya ce ɗaukar matakin zai taimaka wurin hana al’umma faɗa wa cikin ribatar shaiɗanu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here