Ladi Bako, matar gwamnan jihar Kano na farko, Alhaji Audu Bako, ta rasu, a ranar Laraba da ta gabata.
Ɗiyarta Zainab Bako ce ta tabbatar da labarin rasuwarta ta, inda ta ce Hajiya Ladi Bako ta rasu ne a Asibitin Prime Specialist dake Kano bayan ta yi fama da doguwar jinya. ta rasu ta na da shekaru 93 a duniya.
KU KUMA KARANTA: Sarkin Dutse Mai martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi ya rasu a Abuja
An yi jana’izar ta ne a fadar mai martaba sarkin Kano, Kofar Kudu. A cikin birnin Kano. An naɗa marigayi Alhaji Audu Bako gwamnan soja a tsohuwar jihar Kano daga Mayu 1967 zuwa Yuli 1975.
Ya gudanar da gyare-gyare da kuma gina cibiyoyi a fadin jihar.
[…] KU KUMA KARANTA: Matar gwamnan Kano na farko, Ladi Bako ta rasu […]