No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-Ma

A wani rahoto da muke samu na wata mata mai suna Angela cewa mijin ta ya sake ta, biyo bayan yadda ciyar da ita ya gagare shi.

Mijin nata mai suna Daniel ɗan asalin Jihar Imo ya shaida wa manema labarai a ranar laraban da ta gabata cewa, shi ya yi iya ƙoƙarinsa na wurin ɗaukan nauyin matarsa kuma ya yi ƙira ga iyayen ta da su ma su zo domin haɗa kai dan ciyar da ɗiyar su amma suka yi kunnen uwar Shegu da shi.

Daniel dai ya auri Angela ce a matsayin bazawara bayan rabuwar ta da ainihin mijinta wanda bai bayyana mana dalilin rabuwan nasu ba.

KU KUMA KARANTA: Alamara: Tururuwa ta cinye takardun shaidar kashe kuɗaɗe a asusun inshoran NSITF

Bugu da ƙari ya ƙara bayyana wa manema labarai cewa a mako ɗaya kawai matar tana cinye rabin buhun masara ita kaɗai, idan kuma shinkafa za a girka ita kaɗai kawai take cinye babban kwano ɗaya da rabi daga safe zuwa dare.

A ɓangaren ruwa kuma tana iya shanye ruwa leda biyar na fiyo wata cikin kwana uku kacal. Kifi ko nama kuma ba a maganarsu, a bisa waɗannan dalilan yasa mijin nata ya haƙura da ci gaba da zama da ita.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...