Connect with us

Labarai

Matakan da Limaman Jihar Neja suka ɗauka kan auren marayu 100 da Ministar Mata ke inkari

Published

on

Matakan da Limaman Jihar Neja suka ɗauka kan auren marayu 100 da Ministar Mata ke inkari

Limaman Masallatan Juma’a na Jihar Neja da Kwamitin Malamai da iyayen yara 100 da gwamnati ke son aurar da su, sun ce sun ɗauki matakan da suka ga sun dace na tabbatar da yiwuwar aurarrakin, wanda Ministar Mata ta Najeriya ke ƙalubalanta.

A wata sanarwa da daraktan da ke kula da harkokin addini na jihar ya fitar a yau Juma’a, ta ce masu ruwa da tsakin sun yi taron ne a Minna, inda suka tattauna kan batun umarnin kotu da kuma ƙarar Shugaban Majalisar Dokokin jihar Barista Abdulmalik Sarkin Daji da Ministar Matan ta shigar, kan batun ɗaukar nauyin auren marayu 100 da aka shirya yi a ƙaramar hukumar Mariga.

Batun aurar da ‘yan matan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a Najeriya, wanda Minsitar Matan Uju Kennedy-Ohanenye ta shigar da ƙara kotu don neman a dakatar da yin sa a ranar 24 ga watan Mayu kamar yadda aka tsara tun da farko.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta sa hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

A ganin Ministar, ‘yan matan waɗanda yawanci marayu ne da suka rasa mahaifansu a hare-haren ‘yan bindiga da ya addabi jihar, “wani abu daban suka cancanci a yi musu.” kuma ma’aikatarta na bincike don gano ko su wane ne ‘yan matan 100 da shekarunsu da kuma ko bisa amincewarsy za a yi auren.

Sai dai ko a ranar Juma’a, Minista Uju ta wallafa a shafinta na X cewa ta cimma matsaya tare da Sarkin Kotangora, HRH Alh Mohammed Barau Muazu da Kakakin Majalisar Abdumalik Sarkindaji, kan neman hanyar hadin gwiwa don bai wa ‘yan matan sabuwar rayuwa, amma har yanzu hukuncin Kotun yana nan ba kawar da shi ba.

“Ban janye shari’ata ba har sai mun gudanar da aikin tantance ‘yan matan, sannan za mu sa ‘yan matan su shiga makarantu, da koyar da sana’o’in hannu da kuma karfafa wa ‘ya’ya mata, babban burin ma’aikatarmu shi ne tabbatar da ganin an samar da walwala kuma an tabbatar da bukatun ‘yan matan”.

Sanarwar daraktan harkokin addinan ta ce matakai biyar Limamai da Malamai da Iyayen yaran suka ɗauka kan wannan lamari kamar haka;
1. Za a ɗaura auren marayu 100 a ranar 24 ga Mayu, 2024 kamar yadda aka tsara. Dalili shi ne, babu ta inda auren da aka shirya yi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokokin addininMusulunci.

2. Mahalarta taron sun buƙaci Ministar Harkokin Mata Mrs. Uju ta nemi afuwar jama’a nan da kwana bakwai ko kuma a dauki matakin shari’a a kanta.

3. Taron ya yi ƙira ga Shugaban Najeriya da ya kori Ministar cikin gaggawa domin kauce wa rikicin addini a ƙasar.

4. Taron ya kuma yi ƙira ga ɗaiɗaikun jama’a da ‘yan siyasa da su yi koyi da shugaban Majalisar Dokokin kan irin wannan halayya.

5. A karshe taron ya yi ƙira ga al’ummar Musulman jihar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda domin malamai da shugabannin addinin Musulunci na kan gaba a lamarin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like