Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta yi ƙira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza

0
176

Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza tare da bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin wani abu mai muni.

A yayin wani jawabi da ta yi a Alabama na tunawa da shekaru 59 na “Lahadin da aka Zubar da Jini,” ranar da jami’an gwamnatin jihar suka kai wa masu zanga-zangar kare hakkin jama’a hari a gadar Edmund Pettus da ke Selma, Harris ta ce tsagaita wutar za ta bayar da damar fitar da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma ba da damar shigar da taimakon da ake buƙata a Gaza.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sandan Isra’ila sun kama masu zanga-zangar neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza

Ta ƙara da cewa, “Kuma idan aka yi la’akari da ɗimbin wahala a Gaza, dole ne a tsagaita wuta nan da nan na aƙalla makonni shida masu zuwa, kuma a halin yanzu wannan batu yana kan teburin tattaunawa.”

“Wannan zai ba mu damar gina wani abu mai ɗorewa don tabbatar da cewa Isra’ila ta kasance cikin tsaro da kuma mutunta ƴancin al’ummar Falasɗinu na mutunci da ƴanci na cin gashin kai,” in ji ta.

Leave a Reply