No menu items!

Sample Page Title

Date:

Mataimakin shugaban Najeriya ya buɗe taron gwamnonin yankin tafkin Chadi

Daga Idris Umar, Zariya

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a yau wajen buɗe taron Gwamnonin Yankin Tafkin Chadi karo na biyar da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Taron, wanda Gwamnatin Jihar Yobe ta dauki nauyi, ya hada gwamnonin jihohi takwas daga Najeriya, Kamaru, Chadi da Jamhuriyar Nijar, tare da kungiyoyin jin ƙai da ƙungiyoyin kasa da kasa, domin tattauna matsalolin tsaro da neman hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a yankin

KU KUMA KARANTA:Gwamna Zulum ya canza sunan jami’ar jihar Borno zuwa jami’ar Kashim Ibrahim

A jawabin da ya gabatar a madadin Shugaban Kasa, Shettima ya bukaci a ɗauki matakai masu yawa don yaki da ta’addanci da sauran barazanar tsaro da suka addabi yankin Tafkin Chadi.

Ya jaddada cewa rikice-rikicen da suka addabi yankin tsawon shekaru 15 da suka gabata na bukatar amfani da iko cikin hikima, domin tabbatar da tsaron rayuka da walwalar al’ummar dake ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...