Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya gargaɗi PENGASSAN akan Ɗangote
Daga Jameel Lawan Yakasai
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta fi ƙarfi da tasiri fiye da ƙungiyar ma’aikatan mai ta PENGASSAN.
Yana mai cewa wajibi ne gwamnati ta kare Alhaji Aliko Dangote domin ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Shettima ya ce Dangote ba kawai ɗan kasuwa ba ne, ginshiƙi ne na tattalin arzikin Najeriya wanda ya sadaukar da jarinsa da iliminsa domin bunƙasa ƙasar, don haka irin wannan ɗan ƙasa mai kishin ƙasa yana buƙatar tallafi, ba ƙalubale ba.
KU KUMA KARANTA: Ba za mu sayi man fetur kai tsaye daga Ɗangote ba – Dillalan Man Fetur
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare kamfanonin da ke taimakawa wajen samar da ayyukan yi, rage talauci da ƙarfafa masana’antu a cikin gida.
A cewar sa, irin yadda ake mu’amala da Dangote shi ne ainihin yadda duniya ke kallon martabar Najeriya, don haka babu dalilin barin sa cikin rikice-rikicen siyasa ko matsin ƙungiyoyi.









