No menu items!

Sample Page Title

Date:

Matafiya sun maƙale bayan ambaliyar ruwa ya yi awon gaba da wani gada

Matafiya sun maƙale bayan ruwan ambaliya ya yi awon gaba da babbar gadar da ta haɗa yankin Arewa maso Yamma da yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Gadar wadda ta haɗa jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara da yankin Kudu maso Yamma ta rushe ne ranar Litinin a a Ƙaramar Hukumar Keɓɓe da ke Jihar Sakkwato da kuma Shanga a Jihar Kebbi.

Rushewar wannan muhimmiyar gada a sakamakon mamakon ruwan sama ta hana matafiya daga jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara isa zuwa yankin Kudu.

Hakazalika matafiyan da suka taso daga Kudu maso Yamma zuwa Arewa ta Yamma sun maƙale sun kasa tsallakawa zuwa jihohin guda uku.

A yayin ziyarar gani da ido da ya kai wurin, Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa rushewar gadar za ta haifar da mummunan matsala ga harkokin tattalin arziƙin manoma da ’yan kasuwa a faɗin Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 11 a Neja

Gwamnan ya yi ƙira ga ma’aikatar ayyuka ta ƙasa da ta gaggauta gyara gasar domin kawo ɗauki ga matafiya da sauran al’umma.

“Ina ƙira ga ma’aikatar ayyuka ta ƙasa da ta gaggauta ɗaukar mataki kan wannan al’amari domin samar da mafita ga waɗannan ’yan kasuwa, kasancewar wannan hanya ita ce kaɗai take haɗe jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Neja da yankin Kudancin Najeriya.”

Ya bayyana cewa gadar, wadda ke ƙaramar hukumar Keɓɓe ta Jihar Sakkwato a kan hanyar zuwa Jihar Neja ita ce babbar mahaɗar yankin Arewa maso Yamma da yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...