Masu zanga-zanga na cigaba da gudana a Abuja da wasu jihohi

0
89
Masu zanga-zanga na cigaba da gudana a Abuja da wasu jihohi

Masu zanga-zanga na cigaba da gudana a Abuja da wasu jihohi

Daga Ali Sanni

Masu zanga-zangar ƙuncin rayuwa da rashin gudanar da mulki mai inganci sun cigaba da zanga-zanga a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, Ibadan, Abeokuta da Akure bayan tsagaitawa sakamakon ɓata-gari da suka shiga suka kawo cikas.

Idan zaku tuna, ɗaya ga watan Agusta ne masu zanga-zanga suka fito a jihohi da dama na ƙasar domin nuna damuwar gamai da tsarda rayuwa da matsin tattalin arziki da rashin shugabanci na gari a Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Zanga-Zanga: DSS ta musanta kai samame ofishin NLC

Sai dai wasu ɓata-gari sunyi amfani da wannan damar wajen kawo tashin hankali da sace kayan al’umma wanda hakan ya jawo asarar rayuka da dukiyar al’umma musamman a jahonin Kano da Kaduna inda abun yafi muni.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen daya gabata na 2023 ƙarƙashin jam’iyyar African Action Congress ( AAC) Omoloye Sowore ne ya wallafa hotunan fitowa da cigaba zanga-zangar tasu a yau ta shafinsa na X.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here