Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke wasu mutane uku da suka haɗarda; Cornelius Ememah, Nelson Aghogho da Ufuoma Tunde, bisa zarginsu da yin garkuwa da mutane, fyade, da kuma zambatar mutanen da suka haɗu da su ta Facebook.
An kama waɗanda ake zargin ne a unguwar Ufuoma da ke Ughelli ta arewa a jihar Delta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bright Edafe, ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Twitter a ranar Laraba. Ya ce ɗaya daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su, da ya gan su ya ba da labarin da ya kai ga kama su.
KU KUMA KARANTA:Yadda ‘yan yahoo suka yi garkuwa da abokin ta’asarsu kan kuɗin damfara
A cewarsa, mutanen ukun da ake zargin suna yaudarar ‘yan matan da suka haɗu da su ta Facebook zuwa wani otal, inda suke yi musu fyaɗe, tare da tsare su domin neman kuɗin fansa daga ‘yan uwansu.
Kakakin ‘yan sandan nya bayyana cewa, macen a cikin waɗanda ake zargin ita ce ta kai waɗanda abin ya shafa zuwa otal. Ya zuwa yanzu, ‘yan mata 20 ne suka faɗa hannun ‘yan masu damfarar.