Masu unguwanni 13 sun yi murabus a jihar Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hakimin gundumar Jogana da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, Zannan Kano, Alhaji Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya amince da murabus ɗin wasu masu unguwanni su goma sha uku a ƙasarsa, waɗanda suka yi murabus don ƙashin kansu.
Alhaji Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya bayyana hakan ne a yayi zantawarsa da manema labarai ranar Talata 02 ga watan Satumban 2025.
KU KUMA KARANTA: An dakatar da Hakimi da kansila bisa zargin satar Taransifoma a Gwambe
A gundumarsa ta Jogana da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano.









