Masu Haƙar ƙaburbura sun koka kan ƙarancin alawus da matsalolin maƙabarta a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Masu haƙa ƙaburbura da gyara maƙabarta a Kano sun koka kan ƙarancin alawus ɗin da ake ba su, wanda ya ragu daga N5,000 zuwa N3,000 ko ma ƙasa da haka a wasu lokuta.
Malam Suleiman Mohammed, wani mai haƙar kabari a maƙabartar Tudun Wada, ya bayyana cewa a wasu lokutan ana shafe watanni ba tare da an biya su ba. Ya ce sun kai ƙorafinsu gaban Sarkin Kano, inda aka yi musu alƙawarin duba lamarin.
KU KUMA KARANTA:Matsalar Ruwa Sha: Yaushe dokar ta-ɓacin Gwamnatin Kano za ta fara aiki?
A cewarsa, aikin haƙa kabari yana da hatsari kuma yana da buƙatar ƙarfi, don haka yana da kyau a inganta alawus ɗinsu. Bugu da ƙari, ya koka kan yadda ɓata gari ke amfani da maƙabarta wajen shaye-shaye da adana makamai kamar yanda ya shidawa wakilin Jaridar Neptune Prime.
Ya nemi a inganta ayyukansu ta hanyar tsaftace maƙabartar da gyara katangarta da sanya fitulu.