Masu gurasa sun yi zanga-zanga kan tsadar fulawa a Kano

Masu sana’ar gurasa a Jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin jin daɗinsu kan yadda fulawa ta yi tsada a jihar.

A cewar Shugabar Ƙungiyar Masu Sana’ar Gurasa, Fatima Auwal Chediyar ‘Yan Gurasa, ta ce sun shiga yajin aiki har sai farashin fulawa ya daidaita a jihar.

“Farashin fulawa wadda ita ce kashin bayan sana’armu ta yi tsada, kullum idan muka je saya farashi na ƙaruwa, farashin buhun a yanzu ya kai naira 40,000, me za mu yi?”

Ta bayyana cewa, galibin masu sana’ar mata ne marasa aure da ke ɗaukar nauyin iyalansu, inda ta ce hakan na barazana ga rayuwarsu.

“A baya muna karɓar fulawa a kan bashi, muna biya bayan mun sayar amma a yanzu hakan ba ya samuwa.

KU KUMA KARANTA: Bayan ya rage farashin siminti, kamfanin BUA ya ƙara farashin sukari, fulawa, da spaghetti

“Dalilin wannan zanga-zangar ta lumana ita ce, jawo hankalin hukumomi cewa muna fuskantar babbar matsala, nan gaba kaɗan ba za mu iya kasuwanci ba idan ba a yi wani abu a kai ba.”

Ta kuma jaddada cewa ba su da wani zabi da ya wuce su daina kasuwancin su zubawa sarautar Ubangiji ido.

“Yawancin mutane masu ƙaramin ƙarfi suna amfani da gurasa a maimakon burodi don haka ba mu kaɗai hakan za ta shafa ba, har da talakawa da suka dogara da mu.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *