No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya (AMBCN) ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukanta daga yau 27 ga watan Fabarairu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mansur Umar, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan matsaya ce bayan kammala wani taron gaggawa na musamman da ta ƙira domin matsa wa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakin sauƙaƙa kasuwancin masu sarrafa fulawa a ƙasar.

Sanarwar ta ce duk wasu ayyukan haɗawa ko sayar da burodi ya kawo ƙarshe ne a jiya Litinin, 26 ga wata, kuma yajin aikin zai ci gaba har nan da mako ɗaya.

Wannan dai zai ƙara dagula lamurra a ƙasar, daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC) ta kira zanga-zanga ta gama-gari.

KU KUMA KARANTA: Yadda wani mutum ya kashe matar sa saboda burodi

Najeriya dai na fama da tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ya kai ga masu kamfanoni ƙara farashin kayan da suke samarwa sanadiyyar hauhuwar farashin kayan da suke amfani da su.

Fulawa na ɗaya daga cikin kayan masarufi da farashinsu ya yi tashin gwauron-zabi tun bayan da ƙasar ta shiga cikin halin tangal-tangal na tattalin arziƙi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...