No menu items!

Sample Page Title

Date:

Masu garkuwa da mutanen da suka sace Sarkin Fili da ke unguwar Mpape a ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun lakaɗa wa basaraken duka har ya suma kan rashin cikar kuɗin fansa da iyalansa suka biya.

Ku tuna cewa an sace basaraken, Peter David tare da matarsa, ‘ya’yansu uku, da kuma wasu mazauna garin huɗu, yayin da aka kashe mutane biyu.

Da take zantawa da Daily trust a ranar Talata, 5 ga watan Disamba,  Matar Sarkin, Aisha Peter, wadda aka sake ta bayan kwanaki biyu domin ta neman kuɗin fansa N100m, ta ce masu garkuwa da mutane sun yi wa mijin nata dukan tsiya saboda rashin samun kuɗin da ta yi kuɗin da ta tara N8m ne kawai.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna

“Na kira su ta waya da safiyar yau domin sanar da su cewa N8m ne kawai na samu, kuma da na buƙaci na yi magana da shi, ‘yarmu ‘yar shekara 14 ce ta iya magana, sai ta ce min mijina ya ƙasa magana sakamakon duka,” ta bayyana.

An kuma ƙara da cewa, babu ɗaya daga cikin mazauna garin huɗu da aka yi garkuwa da su da masu garkuwan suka ƙubutar da su, waɗanda suka sanya wa kowannen su kuɗin fansa N50m.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...