Masu garkuwa da fasinjoji jirgi a Edo na buƙatar Naira miliyan 20 kan ko wane fasinja

0
509

Waɗanda suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa na Igueben na ranar Asabar sun tuntuɓi wasu ’yan uwan waɗanda lamarin ya shafa inda suka ce suna neman Naira miliyan 20 ga kowanne mutum guda da suka kama.

Wani ɗan unguwar ya shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro ne suka sanar da shi labarin na baya-bayan nan, sai dai jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan, DSP Chidi Nwabuzor ya ce zai yi aiki kan bayanin don tabbatar da ko gaskiya ne.

Sai dai Babban Daraktan, kungiyar cigaban matasan yankin Esan, Benson Odia a lokacin da yake tabbatar da rahoton, ya bayyana cewa buƙatar ta masu garkuwar ba ta dace ba, yana mai kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen kuɓutar da mutanen da aka sace da har yanzu suke tsare a hannun waɗanda suka sace su.

KU KUMA KARANTA:Dubun wata mace da ta ƙware a garkuwa yara ta cika

Ya ce, “Zan iya gaya muku cewa masu garkuwa da mutane sun buƙaci naira miliyan 20 akan ko wane fasinja, jimilar naira miliyan 620 ke nan, wannan wauta ce kuma ban san inda talakawa za su iya tara wannan adadi na kuɗi ba.” In ji shi.

Leave a Reply