Masu Biredi a Najeriya na shirin tsunduma yajin aiki saboda tsadar kayan hada Biredi

0
79

Masu kamfanonin Biredi a Najeriya sun ce suna daf da rufe kamfanoninsu saboda matsalar tashin gwauron zabi da kayan sarrafa Biredin ke yi a halin yanzu.

Biredi dai na ɗaya daga cikin abinci mafi sauƙi da al’ummar Najeriya ke amfani da shi a rayuwarsu ta yau da kullum.

A wani taron manema labarai a birnin Lokoja fadar gwamnatin jihar Kogi, Shugaban ƙungiyar masu buga Biredin a jihar Kogin, Cif Adeniyi Bamidele Gabriel, ya ce shugaban ƙungiyar masu kamfanonin Biredi a Najeriya, Alhaji Munsir Umar, da kuma babban sakataren ƙungiyar sun amince da su tsunduma yajin aiki daga ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu idan har gwamnati ba ta yi ƙoƙarin shawo kan matsalolin tsadar kayan da suke amfani da su ba.

KU KUMA KARANTA:Ba za mu iya ci gaba da biyan kuɗin tallafin wutar lantarki ba – Gwamnatin Najeriya

Haka zalika masu buga Biredin sun koka akan tsawwala masu haraji daga gwamnatin Najeriya.

Shugaban kamfanin Shukura Bread a Najeriya, Alhaji Lawali Shukura, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar a yankin Arewacin Najeriya, yace akwai buƙatar hukumomin Najeriya su yi wani abu cikin gaggawa akan lamarin Biredin da ke da matuƙar tasiri a rayuwar talakawa.

Wannan mataki na masu Biredin dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a kan matsalar tsadar rayuwa al’marin da gwamnatin Najeriya tace tana ƙoƙarin shawo kan shi.

Leave a Reply