Masu amfani da kafafen sada zumunta za su fara biyan haraji a ƙarƙashin sabuwar doka — Gwamnatin Najeriya 

0
145
Masu amfani da kafafen sada zumunta za su fara biyan haraji a ƙarƙashin sabuwar doka — Gwamnatin Najeriya 
Taiwo Oyedele

Masu amfani da kafafen sada zumunta za su fara biyan haraji a ƙarƙashin sabuwar doka — Gwamnatin Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, kuɗaɗen shiga da ƴan Najeriya ke samu ta hanyar aiki daga gida da kuma shahararrun masu amfani da kafafen sada zumunta, ko kuma shigo da kaya, za su fara biyan haraji a ƙarƙashin sabbin dokokin haraji da za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Sauye-sauyen Haraji, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani zaman wayar da kan jama’a game da haraji da cocin Redeemed Christian Church of God (City of David), Lagos ta shirya.

A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta a jiya, Oyedele ya ce ƴan Najeriya da ke aiki daga nesa ga kamfanonin ƙasashen waje, doka ta wajabta musu su bayyana kudin shigar su sannan su biya haraji a Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta fara karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu

“Idan kai ma’aikacin nesa ne, kai dai ma’aikaci ne, sai dai kana aikin ka daga nesa. Kana aiki ga wani kamfani, watakila na Amurka, ko Turai, ko ko’ina.

Kana karɓar albashi. Wannan kuɗin da aka biya maka albashinka ne. Kai da kanka za ka bayyana shi. Domin idan ma’aikacinka yana Najeriya, shi zai cire maka haraji ya biya a madadinka. Amma saboda kamfaninka ba ya Najeriya, ba ya kula da tsarin harajin Najeriya.”

Oyedele ya ƙara da cewa, duk wani ma’aikacin nesa da bai bayyana kudin shigar sa ba, gwamnati za ta gano shi, ta ɗora masa haraji da tara da kuma riba saboda jinkirin biyan haraji.

Ya ce wannan tsarin har ila yau ya shafi masu tasiri a kafafen sada zumunta.
“Haka yake ma ga masu tasiri a kafafen sada zumunta. Kana yin tasiri a yanar gizo, ka na samun kuɗi, dole ka biya haraji,” in ji shi

Leave a Reply