Daga Shafa’atu Dauda, Kano
A ranar Jumu’a da misalin ƙarfe 10:00 na dare wasu ɓata-garin masu ƙwacen waya da ke yawo a babur suka tare Musa Sani Aliyu (Khan) tare da nufin karɓan wayar dake aljihunsa.
A lokacin Musa ya fito daga wurin aikinsa Jalla Radio da nufin tsare abin hawa zuwa gida.
KU KUMA KARANTA: An yankewa mahaifiya hukuncin ɗaurin rai da rai, bisa laifin kashe ‘yarta
Lamarin ya faru ne a daidai ofishin kwastom dake ‘club road’, inda suka yi yunƙurin caka masa wuƙa a ciki, amma Allah ya kiyaye, abin ya same shi a hannu. Wakiliyar Neptune Prime ta zanta da Musa, ga abin da ya ce “zuwa yanzu Alhamdulilh an gyara ciwon an ɗinke min, sai dai raɗaɗin da yatsa na yake yi, ina rokon Allah waɗanda suka min wannan mummunan aikin Allah ya sakamin, Allah ya isar min akan su, domin shi ne maganin duk wani azzalumi. Duk da haka ba su yi nasarar ƙwace wayar ba a hannuna”
[…] KU KUMA KARANTA: Masu ƙwacen waya sun yi yunƙurin hallaka ɗan Jarida a Kano […]