Rundunar ’yan sanda ta kama wasu mutum uku da ake zargin su da fashi da makami da kuma ƙwacen motoci a Abuja.
Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Garba Haruna, yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan ya ce an kama su ne bayan wani ɗauki-ba-dadi da jami’an rundunar.
Ya ce mutanen ukun na da alaka da yawaitar fashi da makami da ƙwacen mota Abuja.
“An kama su da motoci biyu; Toyota Corolla mai launin toka mara lamba da baƙar Toyota Camry 206, ita ma ba ta da lamba, da kuma bindiga guda ɗaya,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA : Yadda za ka kare kanka daga masu ƙwacen Whatsapp
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano ragowar da suke aikata laifukan.
Ya kuma tabbatar wa mazauna Abuja cewa, rundunar ’yan sandan na ci gaba da jajircewa wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali.
Kazalika, ya buƙaci mazauna Abuja da su kasance cikin shiri da bayar da rahoton gaggawa ga ’yan sanda ta wadannan lambobi domin kai musu ɗauki 08032003913, 08061581938, 07057337658.38.