Masarautar Zazzau ta dakatar da basarake kan yi wa matashi hukunci

Majalisar masarautar Zazzau ta amince da dakatar da Marafan yamman Zazzau bayan wani zama da ta yi a ranar Litinin.

A wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Ƙwarbai, ta ce matakin ya biyo bayan samun basaraken da laifin ɗaukar doka a hannun shi.

Sanarwa ta ƙara da cewa: “A sakamakon haka, Majalisar Masarautar Zazzau ta amince cikin gaggawa da dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidu, Marafan Zazzau daga masarautar har sai abin da hali ya yi.”

KU KUMA KARANTA: An kori Dogarin Masarautar Zazzau da ake zargi da yiwa wata mace fyaɗe

Dakatarwar, kamar yadda sanarwar ta nuna ta biyo bayan koken da al’ummar Unguwar Magajiya da ke cikin birnin suka kai wa majalisar.

Masarautar ta ce a shirye take ta ɗauki tsauraran matakai kan masu riƙe da muƙamai waɗanda ke saɓa wa doka, inda ta buƙace su da su miƙa duk wani batu da ya shafi hukunci ga mahukunta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *