Masarautar Katsina ta naɗa sabbin Hakimai 6, ciki har da ɗan Gwamna Raɗɗa

0
443
Masarautar Katsina ta naɗa sabbin Hakimai 6, ciki har da ɗan Gwamna Raɗɗa
Fadar Sarkin Katsina

Masarautar Katsina ta naɗa sabbin Hakimai 6, ciki har da ɗan Gwamna Raɗɗa

Masarautar Katsina ta tabbatar da naɗin sabbin Hakimai guda shida (6), ciki har da Muhammad Dikko Umar Radda, ɗan Gwamnan Jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda, wanda aka naɗa a matsayin Hakimin Raɗɗa.

Sanarwar naɗin ta fito ne daga sakataren masarautar Katsina, Alhaji Bello M. Ifo (Sarkin Yakin Katsina), inda ya bayyana cewa an amince da naɗin sabbin Hakiman a ranar 2 ga watan Agusta, 2025.

KU KUMA KARANTA: Da ni ake haɗa baki, ake garkuwa da mutane a jihar Katsina – Hakimin Runka (Bidiyo)

Ga jerin sabbin Hakiman da aka tabbatar kamar haka:
1. Alhaji Sanusi Kabir Usman – Hakimin Shinkafi
2. Alhaji Ahmad Abdulmumini Kabir Usman Dan-Majen Katsina (Hakimin Dankama)
3. Sanata Hadi Sirika – Marusan Katsina (Hakimin Shargalle)
4. Alhaji Abubakar Dardisu, FCNA, Mni – Hakimin Muduru
5. Alhaji Gambo Abdullahi Dabai – Dausayin Katsina (Hakimin Dabai)
6. Alhaji Muhammad Dikko Umar Radda (Gwagwaren) Katsina (Hakimin Raɗɗa)

Sanarwar ta ƙare da fatan alheri da zaman lafiya ga sabbin masu sarautar, tare da addu’ar Allah ya ba su nasara a jagorancin al’umma.

“Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, amin,” inji Alhaji Bello M. Ifo.

Leave a Reply