Masarautar Kano ta umarci dukannin hakimai da Ƴan Majalisar Sarki da su shigo birnin Kano domin gudanar da hawan sallah
Daga Jameel Lawan Yakasai
Masarautar Kano ta Kofar Kudu ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi II ta umarci dukkan Hakimai da ke ƙarƙashinta su shigo cikin birnin Kano domin halartar Hawan Babbar Sallah.
Wannan na cikin wata sanarwa da fadar masarautar ta fitar a daren Litinin, inda ta bukaci Hakiman su tabbatar da isowarsu cikin lokaci domin tsara jerin hawan Sallah yadda ya kamata.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Kano, sun gayyaci Shamakin Kano kan zargin saɓa wa umarnin haramta hawan sallah a jihar
Sanarwar ta jaddada cewa wannan umarni ya shafi dukkan masu rike da sarautar gargajiya a cikin Masarautar Kano ta Kofar Kudu.
Bikin Hawan Sallah al’ada ce mai muhimmanci wadda ke tattare da nuna haɗin kai da al’adun gargajiya a tsakanin masarauta da al’ummar gari, inda Sarki da Hakimansa ke gudanar da jerin gwano bayan kammala sallar Idi da wasu ranakun da suke biyo bayan ranar Sallah.









