Masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin sarakai 6

Masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin wasu sarakai shida a yankin Hakimin Galambi.

Jami’in yaɗa labaran masarautar, Babangida Hassan Jahun ya ce majalisar masarautar ta soke naɗin sarakan da abin ya shafa ne saboda Hakimin Galambi bai bi ƙa’ida ba wajen naɗa su.

Ya ƙara da cewa masarautar ta dakatar da Haikimin ne Hakimin Galambi, Alhaji Shehu Adamu Jumba daga yin naɗin sarauta na tsawon shekara guda, daga ranar 7 ga watan Nuwamba, sannan wajibi ne ya bi ka’ida nan gaba wajen yin naɗin sarauta.

KU KUMA KARANTA: Masarautar Adamawa ta tuɓe Hakimin Ribadu

A kwanakin baya ne Hakimin Galambi wanda shi ne Ɗanlawal na Bauchi, ya yi wa wasu mutanen shida naɗin sarautar Galadaman Danlawal, Wakilin Dokan Danlawal da kuma Majidadin Danlawal.

Sauran su ne Wakilin Gonan Danlawal, Sarkin Dajin Danlawal da kuma Hardon Danlawal.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *