Masarautar Adamawa ta tuɓe Hakimin Ribadu

0
194

Majalisar Masarautar Adamawa ta tuɓe rawanin Hakimin Ribadu da ke ƙaramar hukumar Fufore da ke jihar, Alhaji Gidado Abubakar.

Muƙaddashin Sakataren masarautar, Alhaji Kabiru Bakari, na ya sanar da hakan a cikin wata takarda da ya aike wa tuɓaɓɓen hakimin.

“Majalisar Masarautar Adamawa ta umarce ni da in rubuta in kuma sanar da kai cewa Gwamnan Jihar Adamawa ya amince da korar ka.

KU KUMA KARANTA: An dakatar da Sarkin Sasa kan rashin biyayya

“Ka mika duk wasu takardun hukuma da ke hannunka, ciki har da takardar shaida, ga Muƙaddashin Sakataren Masarautar Adamawa da ke Yola,’’ in ji wasikar.

Leave a Reply