Masarauta: Ba mu da fargaba kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara – Gwamnatin Kano

0
5
masarauta:%20Ba%20mu%20da%20fargaba%20kan%20hukuncin%20%C9%97aukaka%20%C6%99ara%20-%20Gwamnatin%20Kano%0A%0A%20

Masarauta: Ba mu da fargaba kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara – Gwamnatin Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cikakken bayani kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke game da takaddamar sarautar Kano, domin gyara kuskuren fahimta da rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.

Da yake magana a taron manema labarai da aka gudanar a harabar kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a Kano, Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Isa Dederi, ya jaddada muhimmancin samun ingantaccen bayani dangane da shari’ar da ke gudana.

Barista Dederi ya bayyana cewa Kotun Daukaka Kara, a hukuncin da ta yanke a ranar 10 ga Janairu, 2025, ta tabbatar da soke dokar majalisar masarautu ta Kano ta 2019, tare da soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke a baya.

Sai dai ya bayyana cewa, Alhaji Aminu Babba Dan’Agundi, wanda bai gamsu da hukuncin ba, ya daukaka kara zuwa Kotun Koli ta Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yi kan rikicin Masarautar Kano

Ya kara da cewa hukuncin Kotun Daukaka Kara yana nan daram kuma yana da inganci har sai Kotun Koli ta yanke hukunci akansa.

Ya bayyana dakatar da aiwatar da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yi a matsayin matakin doka na kowa da kowa domin tabbatar da cewa komai ya tsaya cak har sai an yanke hukunci a Kotun Koli.

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci al’umma da su kasance cikin kwanciyar hankali, su zama masu bin doka da oda, tare da gujewa duk wani abu da zai haddasa fitina ko rikici.

Haka kuma, gwamnati ta umarci tawagar lauyoyinta da su nazarci sakamakon shari’ar tare da fitar da mataki na gaba bisa doka.

A madadin Gwamna, Babban Lauyan Jihar Kano ya gode wa al’ummar Kano bisa hakuri, fahimta da kuma addu’o’insu na zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki daya.

Leave a Reply