Masar na buƙatar taimako saboda rikicin Gaza — EU

0
233

A sakamakon ɓarkewar yaƙi a tsakanin Isra’ila da Hamas a zirin Gaza, Majalisar Tarayyar Turai na yunƙurin nema wa Masar talllafin da za a yi amfani da shi wajen agaza wa waɗanda iftila’in ya rutsa da su.

“Masar na buƙatar ɗauki, don haka ya kamata a taimaka mata,” inji Michel.

Michel ya yi wannan maganar ce a yayin da yake halartar wani muhimmin taro a Washington tare da shugaban Amurka Joe Biden da kuma shugabar Kwamitin Gudanarwar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen.

Michel ya kuma ƙara da cewa zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi a ziyarar da zai kai ƙasar a ƙarshen mako.

Bugu da ƙari, a yayin ziyarar, Michel zai halarci taron da Al-Sisi ya gayyace shi wanda za a tattauna batun halin da Gabas ta Tsakiya da Falasɗinu ke ciki da kuma hanyoyin samun zaman lafiya.

Da ma dai tun a farkon wannan mako ne Von der Leyen a Tirana ta sanar da cewa za a bude kofar samar da kayan agaji a zirin Gaza.

Leave a Reply