Marasa lafiya sun soma mutuwa, yayin da asibiti ɗaya tilo na cutar kansa a Gaza ya daina aiki

0
182

Marasa lafiya huɗu sun mutu bayan asibitin Turkish-Palestinian Friendship, wanda shi ne ɗaya tilo da ke kula da masu ɗauke da cutar kansa a Gaza, ya daina aiki.

“Mutum huɗu da ke fama da cutar daji sun mutu yau bayan Asibitin Turkish-Palestinian Friendship ya daina aiki saboda rashin fetur,” a cewar daraktan asibitin, Subhi Skaik, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency.

Ya ƙara da cewa: “Mutanen sun mutu ne sakamakon rashin isassun kayan aiki na asibiti.”

A cewarsa, an ɗauke dukkan masu fama da cutar kansa daga asibitin zuwa Asibitin Dar al Salam da ke Khan Yunis a kudancin Gaza.

Leave a Reply